2019-07-08 20:58:10 cri |
A jiya ne aka bude taron kolin kungiyar kasashen tarayyar Afirka (AU) a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijer, inda aka sanar da fara aiki da yankin cinikayya cikin 'yanci na babbar nahiyar Afirka. Game da wannan batu Geng ya ce, a cikin shekaru kusan 10 da suka gabata, kasar Sin ta yi ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta kasashen Afirka, ta kuma dauki matakai masu yakini a fannonin hada sassan kayayyakin more rayuwa da samar da saukin cinikayya, inganta masana'antu da dai sauransu, kana ta tsaya tsayin daka wajen goyon baya kasashen Afirka da su raya kasashensu bisa karfin kansu, da raya yankin cinikayya cikin 'yanci. Geng ya kara da cewa, fara aiki da yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka ya bude wata sabuwar makoma ga hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Bilkisu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China