Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba ta tsoron duk wani barazana ko tsoratarwa
2019-08-26 19:22:15        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokiin wajen kasar Sin, Geng Shuang ya bayyana cewa, kasarsa ba ta tsoron duk wani barazana ko tsoratarwa. Geng ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, don mayar da martani kan sanarwar da Amurka ta yi na kara haraji kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 550.

Kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka da kar ya yiwa yanayin bahaguwar fahimta, kana ya gaggauta dakatar da wannan mataki maras ma'ana.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce, kasar Sin ta sanar da sanya karin haraji na kaso 10 cikin 100 ko kaso 5 cikin 100 kan kayayyaki 5,078 da ake shigo da su kasar Sin daga Amurka, da darajarsu ta kai dala biliyan 75, domin mayar da martani kan sanarwar da Amurka ta yi a farkon wannan wata na sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin da ake shigo da su cikin kasarta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China