Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasa da kasa sun dauka cewa ya dace Sin ta mayar da martani kan cin zarafin cinikin Amurka
2019-08-25 16:07:39        cri

Kwanan baya gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, za ta kara sanya harajin kaso 10 cikin dari kan kayayyakin kasar Sin da za ta shigo da su kasar wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 300, matakin da ya tilastawa gwamnatin kasar Sin ta dauki matakin mayar da martani a ranar 23 ga wata, kana a jiya 24 ga wata, Amurka ta sake sanar da cewa, za ta kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin da za ta shigo da su kasar wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 550, kasar Sin ta yi adawa kan batun da kakkausar murya.

Yawancin kwararru da al'ummun kasa da kasa suna ganin cewa, ya dace kasar Sin ta dauki matakin mayar da martani kan cin zarafin da Amurka take yi gare ta, saboda ba ma kawai takaddamar cinikayyar da Amurka ta tayar da ita ta lalata moriyar kasar Sin ba ne, har ma ta lalata moriyar kanta, har ta kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin duniya, ya kamata Amurka ta canja tunaninta ta daidaita matsalar ta hanyar yin tattaunawa.

Tsohon shugaban hukumar tsara manufofin tattalin arziki da kasuwanci ta birnin London na kasar Birtaniya John Ross ya gayawa manema labaran kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ta Email cewa, mayar da martanin da kasar Sin ta yi, mataki ne mai dacewa da ta dauka bayan da Amurka ta kara sanya mata harajin kwastam ba tare da bayyana dalili ba.

Shugaban kungiyar wake ta Amurka David Stephens ya bayyana cewa, a cikin shekara guda daya da ta gabata, kungiyar waken kasar ta dinga yin kira ga gwamnatin Amurka da ta daina yin takaddamar cinikayya da kasar Sin, saboda takaddamar ta kawo mummunan tasiri gare su yayin da suke sayar da wake, har ta sa manoman waken Amurka sun shiga mawuyacin hali, yanzu haka adadin waken da suke ajiyewa yana kara karuwa saboda akwai wahala su sayar da su ga masu sayayya.

Masanin harkokin kasa da kasa na kasar Kenya Edhurley Cavens yana mai cewa, hadin kai zai amfamawa sassan biyu, amma yaki zai lalata moriyarsu duka, har kullum gwamnatin kasar Sin ta nace ga matsayin warware matsala ta hanyar yin tattaunawa, a don haka ya dace Amurka ta canja tunaninta, saboda daukacin kasashen duniya suna fatan Sin da Amurka za su daidaita takaddamar ta hanyar yin tattaunawa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China