Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi Allah wadai da matakin Amurka na ayyana Sin a matsayin mai rage darajar kudi
2019-08-06 19:12:03        cri

Babban bankin al'umma na kasar Sin, ya bayyana matukar rashin jin dadin kasarsa game da shawarar da baitul malin Amurka ya yanke, na ayyana kasar a matsayin "mai rage darajar kudi".

Wata sanarwa da babban bankin na kasar Sin ya fitar, ta bayyana cewa, daukar wannan mataki kan kasar Sin bai dace da nagartattun matakan da har za a bayyana a matsayin "rage darajar kudi" da baitul malin na Amurka ya gindaya ba.

Sanarwar ta kara da cewa, matakin Amurka wani tsari ne na kashin kai da ba da kariya, kuma hakan ya kawo illa matuka ga dokokin kasa da kasa, zai kuma yi mummunan tasiri ga tattalin arziki da ma kasuwannin kudi na duniya.

Don haka, babban bankin kasar Sin na kira ga Amurka, da ta hanzarta janye wannan mataki tun kafin lokaci ya kure, sassan ta koma bisa turba cikin adalci.

Sanarwar ta ce, raguwar darajar kudin, alama ce ta irin kayayyakin dake shiga kasuwa da bukatan masu sayayya gami da kwan gaba kwan bayan da ake fuskanta a kasuwanni musayar kudaden ketare na duniya, sakamakon sauye-sauyen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta da kuma karuwar tankiyar cikiyayya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China