Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka ta daina fakewa da addini tana tsoma mata baki cikin harkokin gida
2019-07-20 15:34:45        cri

Kasar Sin ta yi kira ga Amurka, ta mutunta bayanai na gaskiya, ta kuma yi watsi da zargi, kana ta daina amfani da batutuwan addini tana tsoma mata baki cikin harkokinta na cikin gida.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce mataimakin shugaban Amurka Mike Pence da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, sun soki tsarin da 'yancin bin addini na kasar Sin a wani taron da Amurka ta yi kan 'yancin bin addini.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, Geng Shuang ya ce jawaban Mike Pence da Mike Pompeo game da kasar Sin na rikitar da jama'a da kuma tauye gaskiya, yana mai cewa, tuni Sin ta gabatar da korafinta kan batun ga Amurka.

Ya kuma bayyana cewa, al'ummar kasar Sin na more 'yancin bin addini bisa dokokin kasa, kuma gwamnatin kasar na kare 'yancin bin addini da hakkokin da suka jibance shi na al'ummarta.

Ya ce gina cibiyoyin ba da horon sana'o'i a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta, ingantacciyar hanya ce ta tabbatar da hakkoki, ciki har da hakkin dogaro da kai da kuma ci gaba na al'ummar jihar Xinjiang.

Ya kuma bukaci Amurka ta daina gabatar da jawabai na karya da ba su da tushe, wadanda suka kaucewa gaskiya kuma suka saba da tunani. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China