Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana maraba da kasashe daban daban don zuba jari da gudanar da cinikayya a kasar
2019-08-26 15:13:12        cri
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, ya yi bayani a yayin da yake halartar bikin baje koli na sana'ar kwaikwayon tunanin dan Adam na kasa da kasa na kasar Sin karo na 2 da har yanzu ake yi a birnin Chongqing na kasar, inda ya ce, kasarsa na maraba da masu cinikayya na kasashe daban daban, ciki har da kasar Amurka don su zuba jari da gudanar da harkoki a kasar ta Sin, kasar Sin za ta ci gaba da samar da muhallin zuba jari mai kyau, da kiyaye ikon mallakar fasaha, da tsayawa kan bude kofa wajen inganta sana'ar kwaikwayon tunanin dan Adam, kana da adawa da kafa shinge a fannin fasaha da ra'ayin bada kariyar ciniki. Liu ya kara da cewa, kasar Sin tana son nuna ra'ayin kai zuciya nesa wajen warware matsaloli ta hanyar yin shawarwari, da tsayawa kan kara tsanantar yakin cinikayya. A ganin kasar Sin, yakin cinikayya ba ya amfani kan moriyar kasar Sin, da ta Amurka har ma da ta jama'ar duniya baki daya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China