Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ningxia yankin da ya fi ko wane samar da madara a kasar Sin na shirin kara habaka sanaar kiwo
2019-08-26 13:35:19        cri

Jihar Ningxia dake arewa maso yammacin kasar Sin mai cin gashin kanta, ta fitar da wani shiri na kara inganta sana'ar samar da madara da dangoginsa, da nufin kara habaka gonakin dake da sama da shanu 100, ta yadda za su mamaye fiye da kaso 99 na jimilar gonakin jihar, ya zuwa shekarar 2022.

Burin jihar Ningxia da ya fi kowane samar da madara a kasar Sin shi ne, kara yawan danyen madarar da take samarwa a kowace shekara, ta yadda ya zarce ton miliyan 2.6 ya zuwa shekarar 2022, sannan amfani da takin da ake samu daga dangogin madara ya kai kaso 92.

Jihar za ta karfafa gwiwar manyan gonakin kiwo su rungumi tsarin noma mai kiyaye muhalli da kuma amfani da rufaffun kayayyakin aiki domin zamanintar da sana'ar.

Karkashin shirin, Ningxia za ta bunkasa hada samar da harawa da kiwo, bisa ba da muhimmanci ga aikin samar da madara.

Ya zuwa karshen bara, jihar Ningxia na da shanun da adadinsu ya kai 600,000, daya daga cikin adadi mafi yawa a kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China