Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagororin tattaunawa game da cinikayya da tattalin arzikin Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho
2019-07-19 20:02:29        cri

A jiya Alhamis ne mataimakin firaministan Sin, kana mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kuma babban jagoran tawagar Sin a tattaunawar cinikayyar raya tattalin arziki da Amurka Mr. Liu He, ya zanta da wakilin cinikayyar kasar Amurka Robert Lighthizer, da sakataren baitulmalin kasar Steven Mnuchin ta wayar tarho.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafin ta na yanar gizo, ma'aikatar cinikayyar Sin ta ce, kusoshin sassan biyu sun yi musayar ra'ayoyi da tsagin Amurka, game da batun aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, a gefen taron G20 da ya gudana a birnin Osaka na kasar Japan.

Sun kuma tattauna game da mataki na gaba na tattaunawa, da wakilan sassan biyu za su tunkara.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China