Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guraben karo karatu na gwamnatin Sin ya baiwa matasan Najeriya damar cimma buri
2019-08-23 11:08:42        cri

A wata rana da yamma cikin watan Maris na shekarar 2018, wani matashi wanda ya kammala karatunsa na digirin farko mai suna Ebenezer Onyedika, ya samu wani sako ta wayarsa ta hanyar WhatsApp. Sakon wanda daya daga cikin abokansa ya tura masa, yana dauke da wani shafin intanet wanda za'a latsa don neman gurbin karo karatu a kasar Sin. Da farko ya yi watsi da sakon.

Bayan kwanaki biyu da samun wancan sako, kwatsam sai wani dan uwan matashi Onyedika ya kira shi ta waya inda yake ba shi labari game da wata dama ta neman gurbin karo karatu a kasar Sin.

Daga nan ne sai Onyedika ya fahimce wannan sakon wanda hukumar samar da guraben karo karatu ta tarayyar Najeriya ta fitar muhimmi ne, ita dai hukumar tana karkashin ma'aikatar ilmi ta tarayya ne kuma tana bayar da damammakin guraben karo karatu wanda ya kunshi karatun digirin farko, na biyu, da kuma digirin digirgir, karkashin wani shirin yarjejeniyar hadin gwiwa kan sha'anin ilmi a tsakanin kasashen biyu.

Matashi Onyedika yace, "Ban san ta ina zan fara ba, bayan da na bude wannan shafi. Daga bisani na sake samun wani karin kiran wayar daga dan uwana inda ya bayyana mini yadda zan tafiyar da al'amarin. Wannan ya sanya na fahimce cewa al'amarin na gaskiya ne daga nan sai na fara sha'awar nema kuma na cigaba da bin makatan neman bi-da-bi".

Al'amarin ya wuce tunaninsa, domin kuwa tuni bukatar da Onyedika ya gabatar ta samu karbuwa bayan da haye dukkan wata tantancewa da aka gudanar wanda ya kunshi binciken lafiyar dukkan wadanda suka mika bukatar neman gurbin karo karatun.

Yana daga cikin daliban Najeriya 58 wadanda suka samu guraben karo karatu karkashin shirin gwamnatin Sin na samar da guraben karo karatu na shekarar 2019 a jami'o'i daban daban na kasar Sin.

A wannan karo daliban da suka samu nasarar an shirya musu wata muhimmiyar bita a ranar Laraba a ofishin jakadancin kasar Sin dake Abuja, babban birnin Najeriya, daliban sun kunshi masu neman digirin farko su 3, da masu neman digiri na biyu 39, da kuma masu neman digiri na uku su 16.

Wadannan daliban 'yan Najeriya da suka samu nasarar guraben karo karatun a kasar Sin za su tashi daga Najeriyar zuwa Sin a ranar 30 ga watan nan na Agusta, ko kuma a farkon watan Satumba, domin cimma mafarkin da suka jima suna yi a rayuwarsu. Wasu daga cikinsu za su bar gida har tsawon shekaru biyar.

Wadannan guraben karo karatun, gwamnatin kasar Sin ne zata dauki nauyinsa kacokan karkashin wasu shirye shirye daban daban, kamar shirin tallafin kasar Sin ga kasashe masu tasowa, yarjejeniyar Sin da Najeriyar, da kuma na gamayyar kasa da kasa wanda aka samar karkashin taron kolin dandanlin hadin gwiwar Sin da Afrika na Beijing 2018 wato FOCAC.

Ga Onyedika, da mafi yawan daliban da suka samu wannan muhimmiyar damar karo karatu daga gwamnatin Sin sun bayyana cewa, basu da sukunin da zasu iya daukar nauyin karatu a kasashen waje, suna ganin cewa, wannan damar da suka samu ta gurbin karo karatu ya samar musu da gwarin gwiwa wajen cimma muhimman burikan da suke da su a rayuwarsu na samun ingantaccen ilmi a kasar Sin.

Hakika wannan wata alama ce dake kara bayyana irin nasarorin da kasar Sin ta samu karkashin manufofinta na yin gyare gyare a gida da bude kofa ga waje shekaru 40 da suka gabata, ga matashi Onyedika, wanda ya samu gurbin karo karatu a kasar Sin ya bayyaana cewa,"Ina shirin karantar fannin kimiyyar hada sinadarai a jami'ar kasar Sin a matakin digiri na biyu, zan kasance a kasar Sin har tsawon shekaru 2, zan yi karatu na a jami'ar fasaha ta Wuhan".

A cewar matashin mai shekaru 26 a duniya, wanda ya kammala karatun digirinsa na farko a cikin gida Najeriya a fannin fasahar sinadarai a shekara daya da ta gabata ya bayyana cewa, idan ya samu nasarar kammala karatun digirinsa na biyu a fannin fasahar hada sinadarai a kasar Sin, babban mafarkin da yake da shi a rayuwa shi ne, yana son ya kawo sauyi a duniya wajen warware dubun matsalolin dake addabar duniya wadanda suka shafi gurbatar yanayi. Ya ce idan ya kammala karatunsa zai koma Najeriya domin taimakawa kasar da ilmin da ya samu daga kasar Sin.

Ko shakka babu, gwamnatin kasar Sin tana iya bakin kokarinta wajen sauke nauyin dake bisa wuyanta na kara zurfafa mu'amala da kasa da kasa, musamman wajen hadin gwiwarta da kasashe masu tasowa a nahiyar Afrika don bunkasa ilmi, da fasahohin zamani, da kirkire kirkire, domin amfanawa dukkan bil adama a fadin duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China