Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya gasar sada zumunci ta wasan kwallon tebur a tsakanin Sin da Najeriya don murnar bikin kasa mai zuwa
2019-08-05 13:32:50        cri

A kwanan baya, an shirya gasar sada zumunci ta wasan kwallon tebur a tsakanin 'yan wasan kasashen Sin da Najeriya mai taken kofin "October 1" a cibiyar al'adun kasar Sin dake birnin Abujan Najeriya. An shirya gasar ne da nufin murnar cikon shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da cikon shekaru 59 da samun 'yancin kan Najeriya, da kuma cikon shekaru 48 da kafa huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Najeriya, kana da inganta mu'ammalar al'adu a tsakanin kasashen biyu.

An soma shirya irin wannan gasa ta sada zumunci ta wasan kwallon tebur a tsakanin kasashen Sin da Najeriya ne a shekarar 2017, wannan ne karo na uku da aka shirya gasar. Ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya, da sashen kungiyar NUJ ta Najeriya dake Abuja, da kuma jaridar "Leadership" ne suka dauki nauyin shirya gasar. Kana cibiyar al'adun kasar Sin ta Najeriya, da kungiyar kasuwancin kasar Sin dake Najeriya sun ba da taimakon shirya gasar, kuma yawancin masu shiga gasar sun fito ne daga sassan ma'aikatan kafofin watsa labaru na Najeriya, da wasu ma'aikatan kamfanoni da hukumomin kasar Sin dake kasar.

Bayan gasar da aka gudanar, bangaren Najeriya ya yi nasara a fannin namiji da namiji, da gasa ta tsakanin mace da mace, da kuma gasa ta tsakanin maza biyu biyu, bangaren kasar Sin kuma ya lashe gasar ta hadakar maza da mata.

Mashawarci a fannin al'adu na ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya, kuma daraktan cibiyar al'adun kasar Sin Li Xuda ya bayyana cewa,

"Ranar 1 ga watan Oktoba rana ce ta bikin kasa a kasashen Sin da Najeriya, mun hada kai don shirya wannan gasa ne da nufin murnar cikon shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da cikon shekaru 59 da samun 'yancin kan Najeriya, da kuma cikon shekaru 48 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, kana da karfafa zumunci a tsakanin kasashen biyu, da inganta hadin kai a tsakaninsu."

A nasa bangaren, shugaban jaridar "Leadership" ta Najeriya, Abdul Gombe ya bayyana cewa, gasar sada zumunci ta wasan kwallon tebur na da ma'ana kwarai. Ya ce,

"Wannan ne karo na uku da aka shirya irin wannan gasa a gabannin ranar bikin kasa ta kasashen Najeriya da Sin, wadda ta nuna zumunci a tsakanin kasashen biyu. A waje guda kuma tana karfafa lafiyar jikin masu shiga gasar. Ban da wannan kuma, akwai wasu 'yan jarida da dama da suka shiga gasar, wadanda muhimmin aikinsu shi ne, kara inganta mu'amala a tsakanin jama'a da gwamnati. Don haka, ina fatan ganin gasar ta tallafa wajen inganta zumunci a tsakanin jama'ar kasashen Sin da Najeriya."

Zhang Zhenghua, wanda ya zama zakara a gasa ta hadakar maza da mata, ya fito ne daga wani kamfani na birnin Shanghai na kasar Sin, ya yi amfani da damar ziyarar aiki, ya tafi Abuja daga Legos, don shiga gasar. Ya ce,

"Mun zo nan ne musamman ta jirgin sama, domin halartar wannan gasa. Bisa shirin da muka tsara, yanzu kamata ya yi a ce mun riga mun koma Legos, amma mun canja tikitin jirgin saman mu zuwa na daren yau. Ta hanyar wannan 'yar karamar kwallo, an hada jama'ar kasashen Sin da Najeriya, wadanda ke da nisa a tsakaninsu don su taru a wani babban daki, su buga wannan gasa. Ta wannan gasar, ina iya jin zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu, ina fata za a iya shirya ayyuka masu yawa kamar wannan, kuma mu ma za mu sa himma wajen shiga makamantan su." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China