Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala gwajin tashi da saukar jirage a filin jirgin sama na Jieyang Chaoshan
2019-08-22 11:06:12        cri

Hukumar lura da filayen jiragen sama ta lardin Guangdong, ta ce an kammala gwajin tashi da saukar jiragen sama a filin jirage na Jieyang Chaoshan dake lardin na kudancin Sin.

A ranar Laraba ne dai aka kammala wannan aiki, bayan fadada ginin filin jirgin, da nufin mayar da shi cibiyar zirga zirgar jiragen sama ta kasa da kasa.

Bayan fadada filin jirgin, yanzu haka yana iya karbar manyan jiragen sama samfurin Boeing 787, da Airbus 330. Yana kuma baiwa fasinjoji damar tashi zuwa sassan nahiyar Turai da Amurka.

Aikin fadada filin jirgin dai ya kunshi kara tsayin titin tashi da saukar jirage da mita 400, inda a yanzu tsayin titunan sa suka kai mita 3,200, an kuma fadada harabar dake karbar jirage 21 zuwa 40.

Bisa tsarin da ake da shi na bunkasa yankin tattalin arziki na Guangdong zuwa Hong Kong zuwa Macao, tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020, an fara aiwatar da manufar gina filayen tashi da saukar jiragen sama a yankin Guangdong masu matsayi na kasa da kasa, daura da kogin Pearl, matakin da zai haifar da karin yawan filayen jiragen sama a Jieyang, da Zhanjiang da Shaoguan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China