Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ba da tallafin karatu ga dalibai 259 na Tanzania
2019-08-20 09:29:41        cri

Ofishin jakadancin kasar Sin a Tanzania, ya sanar cewa, gwamnatin kasar Sin ta ba da tallafin karatu ga daliban Tanzania 259.

Jakadiyar kasar Sin dake Tanzania Wang Ke, ta ce gwamnatin kasar Sin da jami'o'in kasar ne suka ba da tallafin ga daliban, ta hannun ma'aikatar kula da ilimi da kimiyya da fasaha ta Tanzania.

Jakadiyar ta bukaci daliban su dage wajen karatu a jami'o'in na kasar Sin domin koyon dabaru da ilimin da za su yi amfani da su wajen raya kasarsu, bayan sun kammala karatu.

A nata bangaren, ministar ilimi da Kimiyya da fasaha ta Tanzania, Joyce Ndalichako, ta godewa gwamnati da jami'o'in kasar Sin bisa rubanya adadin wadanda suka ci gajiyar tallafin daga 120 a shekarar 2018 zuwa 259 a bana.

Ministar ta ce, tallafin na da muhimmanci ga ci gaban Tanzania, la'akari da bukatar kasar ta samun kwararrun da za su ingiza ajandarta ta bunkasa ayyukan masana'antu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China