Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mawallafa sun tattauna game da harkar dab'i a kasar Sin
2019-08-20 10:37:19        cri

Mawallafa daga kasashe daban daban, sun gudanar da taron kasa da kasa na baki masu ruwa da tsaki, game da wallafa litattafai a kasar Sin. An dai gudanar da taron ne a jiya Litinin, inda masu ruwa da tsaki a fannin wallafa, suka tattauna game da musayar fasahohi, da koyi da juna tsakanin al'ummu daban daban.

Sama da mutane 200 da suka hada da mawallafa, da kwararru daga sama da kamfanonin dab'i 60, daga kasashe 30 ne suka halarci taro.

Wani jami'in sashen yada manufa na kwamitin kolin JKS ya bayyana cewa, shekarar 2019 shekara ce ta cika shekaru 70, tun bayan kafuwar sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar, kuma cikin wadannan shekaru, akwai labarai masu tarin yawa da za a iya gabatarwa game da Sin. Jami'in ya kuma yi fatan masu ruwa da tsaki a fannin dab'i na cikin kasar Sin da na waje, za su kara azama wajen gudanar da musaya, da hadin gwiwa, karkashin irin labaran da kasar ta samar cikin wadannan shekaru, su kuma ci gaba da gudanar da rubuce rubuce masu tasiri ga kasa da kasa.

A cewar manajan sashen dab'i a kamfanin "Springer Nature" Mr. Niels Peter Thomas, idan har ana son ganin tasirin rubuce rubucen kasar Sin a mataki na kasa da kasa, muhimmin mataki shi ne inganta hadin gwiwa da sauran marubuta na kasa da kasa.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China