Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta dau mataki kan kamfanonin Amurka da suka amince su sayarwa Taiwan makamai
2019-08-22 10:44:14        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce Sin na fatan Amurka za ta yi watsi da kudurin ta na sayarwa yankin Taiwan makamai.

Geng Shuang ya yi wannan kira ne, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Laraba, yana mai cewa, kasar sa za ta dauki matakan da suka wajaba na kare moriyar ta, ciki hadda kakaba takunkumi ga kamfanonin Amurka masu ruwa da tsaki a shirin sayar da makaman.

A ranar Laraba ne dai ma'aikatar tsaron Amurka, ta sanarwa majalissar dokokin kasar a hukumance, shirin da ake yi na sayarwa yankin Taiwan jiragen yaki samfurin F-16 guda 66, tare da sauran kayan ayyukan sarrafa su, da darajar su ta kai dalar Amurka kusan biliyan 8. Kaza lika an tanaji baiwa yankin na Taiwan tallafi a fannin aiki da kayayyakin yakin.

Game da hakan, Mr. Geng ya ce, kasar sa na matukar adawa da wannan cinikayya, ta kuma gabatar da korafin ta ga tsagin Amurka. Ya ce batun yankin Taiwan na da nasaba da ikon mulkin kai, da cin gashin kai, da kuma martabar Sin, wanda hakan babbar moriya ce da Sin ke karewa.

Kaza lika Geng ya bukaci Amurka da ta martaba manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da sauran tanade-tanaden da aka amincewa, cikin yarjejeniyoyi 3, na bayan tarukan wakilan sassan biyu, ta kuma soke batun wancan ciniki na makamai, kana ta dakatar da duk wata alakar ayyukan soji da tsibirin na Taiwan.

Mr. Geng ya ce, idan har Amurka ta ki amincewa da wannan shawara, to kuwa za ta dauki alhakin duk wani mataki da zai biyo baya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China