Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummomin duniya sun bayyana damuwa game da matakin Amurka kan Taiwan
2019-05-10 10:45:11        cri

Majalisar wakilan Amurka, ta amince da dokar da ta tabbatar da kudurin Amurka na hulda da Taiwan, lamarin da ya haifar da damuwa tsakanin al'ummomin duniya.

Ana ganin cewa, matakin na Amurka, katsalandan ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda kuma zai yi illa ga dangantakarta da kasar Sin da kuma zaman lafiya a shiyyar.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, MDD za ta ci gaba da goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya bisa kudurorin da suka dace, ciki har da kudurin majalisar na shekarar 1971.

A cewar Charles Onunaiju, daraktan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Nijeriya, batun Taiwan, batu ne da ya shafi ga kasar Sin da harkokinta na cikin gida, don haka, ya kamata Amurka ta mutunta manufar kasar Sin daya tak a duniya, ta kuma daina duk wani nau'i na takala, kamar samar da makamai ga Taiwan, ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar.

Shi kuwa shehun malami a bangaren huldar kasashen waje na jami'ar Yaounde ta 1 dake Kamaru, Elvis Ngolle Ngolle cewa ya yi, kudurin na majalisar dokokin Amurka ya dasa ayar tambaya game da sahihancin Amurka a wajen kasashen waje, domin ta amince da manufar kasar Sin daya tak a duniya. Kuma bisa sabon matakin da ta dauka, Amurka ta karya alkawari da amana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China