Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar 'yan wasan Najeriya ta tashi zuwa Morocco don halartar gasar wasannin Afrika
2019-08-16 09:21:44        cri

Tawagar wakilan Najeriya ta gasar wasannin Afrika ta shekarar 2019 a jiya Alhamis ta tashi daga Abuja, babban birnin kasar ta dauki shatar jirgi zuwa kasar Morocco, inda za'a gudanar da wasannin daga ranar 19 zuwa 31 ga watan Agusta.

Kimanin 'yan wasa da jami'ai 462 ne za su wakilci kasar ta yammacin Afrika a wasan da za'a buga a Rabat, babban birnin kasar Morocco, Olusade Adesola, babban sakataren ma'aikatar wasannin da ci gaban matasa ta Najeriya ya sanar da hakan.

A ranar Laraba, aka shirya bikin ban kwana da tawagar da za ta wakilci Najeriyar a Abuja.

A yayin bikin ban kwanan, shugaban Najeriya Muhammad Buhari, wanda sakataren gwamnatin tarayya ya wakilce shi, ya bukaci 'yan wasan da su mayar da hankali a wasannin, wanda zai kasance a matsayin share fage na shiga gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta shekarar 2020 a Tokyo.

A sakon da shugaba Buhari ya aike ga tawagar 'yan wasan, ya ce, gwamnatin tarayya a shirye take ta tabbatar da ganin an samu cikakkiyar nasara a gasar wasannin Afrika kuma za'a tabbatar da ba da cikakkiyar kulawar da 'yan wasan ke bukata. Kana ya bukaci tawagar 'yan wasan da su kasance jakadu na gari ga Najeriya a yayin da suke filin wasan har ma da wajen filin wasan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China