Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jirgin kasan Sin ya yi zirga-zirga miliyan 2.4 yayin aikin hajjin bana a Macca
2019-08-15 13:15:00        cri

Kamfanin kera jiragen kasa na kasar Sin CRCC, mai kula da layin dogon jirgin kasa mai zirga zirga a cikin gari yayin aikin hajjin bana a saudiyya, ya kammala jigilar aikin hajjin bana a jiya Laraba.

Yayin kwanaki 7 da ya yi yana aiki, ya yi aikin sa'o'i 156, kuma an yi zirga zirga miliyan 2.4 cikin aminci ba tare da wata matsala ba.

Mataimakin manajan kamfanin, Li Chongyang, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, da farko, an shirya jirage 1,718 ne za su yi zirga zirga a kan layin dogon, sai dai kuma jirage 2,214 ne suka yi zirga zirga a kai.

An yi jigilar mahajjata daga dukkan fadin duniya lami lafiya yayin lokacin aikin hajjin bana da ya shafe kwanaki 5 daga ranar 9 ga watan Agusta, bisa kalandar addinin musulunci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China