Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar tattara bayanan sirri ta Sudan ta kwace tarin makamai a Khartoum
2019-08-04 16:16:13        cri

Hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Sudan (GIS), ta sanar da kwace makamai da alburusai masu tarin yawa, baya ga magunguna nau'ika daban-daban.

Shugaban hukumar GIS, Abu-Bakr Dambalab, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a Khartoum cewa, GIS hukuma ce ta kasar dake aiki bisa kwarewa, yana mai cewa, tana aiki da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ciki har da ta soji.

A ranar 29 ga watan Yuli ne shugaban kwamitin mulkin soji na riko na kasar, Abdel Fattah Al-Burhan, ya ba da umarnin sake fasalin hukumar tsaro da tattara bayanan sirri ta kasar NISS, tare da sauya mata suna zuwa hukumar GIS.

Bayan sojoji sun hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar, Omar Al-Bashir a watan Afrilu ne, 'yan adawa suka bukaci a rushe hukumar ta NISS.

Sai dai, kwamitin soji, wanda ke mulkin kasar, ta dage kan ci gaba da kasancewar hukumar, amma ta amince a sake mata fasali, ta yadda za ta mayar da hankali kan yaki da ta'addanci da cin amanar kasa da yaki da safarar mutane da cin hanci da rashawa.

Bisa kundin tsarin hukumar GIS da kwamitin soji da kawancen 'yan adawa suka cimma, hukumar za ta kasance karkashin majalisar zartarwar da ministoci yayin wa'adin mulkin hadin gwiwa na wucin gadi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China