2019-08-16 10:29:32 cri |
Hadakar kungiyoyin adawar Freedom and Change Alliance ta Sudan sun amince da bayyana sunan Abdalla Hamdok a matsayin wanda za'a nada firaiminista a gwamnatin rikon kwaryar kasar.
A bisa tsarin yarjejeniayar kafa gwamnatin hadaka ta rikon kwaryar da 'yan adawar na Freedom Alliance suka amince da shi, sun yarda a nada Dr. Abdalla Hamdok a makamin firaiministan kasar a tsawon wa'adin shugabancin gwamnatin rikon kwaryar kasar wanda aka tsawaita wa'adin zuwa shekaru uku da wata uku, a cewar kungiyar kwararrun kasar Sudan, wacce babbar jigo ce ta kungiyar Freedom and Change Alliance.
Kungiyar ta yi maraba da zabar Hamdok a matsayin firaiministan kasar, kuma ta tabbatar da yi masa biyayya.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China