Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An dage tattaunawar majalisar sojojin Sudan da 'yan adawa zuwa Lahadi
2019-07-14 15:58:07        cri

Wakilin kungiyar tarayyar Afrika (AU) a kasar Sudan Mohamed Hacen Lebatt, ya sanar a ranar Asabar cewa, an dage tattaunawar sulhu tsakanin majalisar sojojin rikon kwaryar kasar Sudan (TMC), da kungiyar 'yan adawa ta Freedom and Change Alliance, zuwa ranar Lahadi.

"Tattaunawar, wadda da farko aka shirya gudanarwa a ranar Asabar tsakanin TMC da kungiyar Freedom and Change Alliance, an dage zuwa ranar Lahadi," Lebatt ya fadawa manema labaru.

Ya bayyana cewa, an jinkirta tattaunawar ne bisa bukatar da kungiyar 'yan adawa ta Freedom and Change Alliance ta nema domin kara tuntubar mambobinta.

A ranar Juma'a, TMC da 'yan adawar sun bayyana aniyar bin matakan siyasa, wadda ta shafi dukkan hukumomin game da wa'adin mika mulkin kasar.

A ranar 5 ga watan Yuli, TMC da Freedom and Change Alliance, karkashin masu shiga tsakani na kasar Habasha da kungiyar tarayyar Afrika, sun amince da kafa shugabancin rikon kwaryar kasar wanda zai shafi dukkan bangarorin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China