Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Tanzania ya kori ministan kula da muhalli na kasar
2019-07-22 10:00:30        cri
Shugaban kasar Tanzania, John Magufuli, ya kori January Makamba, Ministan ofishin mataimakin Shugaban kasar, wanda ke kula da harkokin muhalli da hadin kan kasa.

Wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar shugaban kasar, Gerson Msigwa ya fitar, ta ce Shugaba Magufuli ya nada George Simbabchawene a matsayin wanda zai maye gurbin January Makamba.

Sanarwa bata bayyana dalilan korar matashin ministan muhallin ba, wanda ya fara haramta amfani da jakar leda a kasar, dokar da ta fara aiki a hukumance a ranar 1 ga watan Yunin bana.

Haramta amfani da jakar leda na da nufin rage bolar robabi da rahotanni suka ce na gurbata teku da kasa, a wani mataki mai tada hankali. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China