![]() |
|
2019-08-10 20:19:00 cri |
Mutane akalla 60 sun mutu a yau Asabar, sanadiyyar faduwar wata tankar man fetur a yankin Morogoro dake da nisan kilomita 200 daga Dar es Salam, babban birnin kasuwanci na kasar Tanzania.
A cewar kwamishinan yankin Morogoro, Stephen Kebwe, wasu mutane 70 kuma sun kone sosai yayin da suke kokarin dibar man dake zubewa daga tankar.
A cewar jami'in, hatsarin ya auku ne da misalin karfe 8 na safiya agogon wurin, inda tankar man fetur da ta fito daga Dar es Salaam take shiga yankin Morogoro, ta fadi, a lokacin da direban ke kokarin kaucewa buge wani mai babur. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China