Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane12 sun mutu sanadiyyar musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da mayakan Boko Haram
2019-08-13 09:12:37        cri

Mayakan Boko Haram 8 da sojoji 2, sun mutu yayin karon batar da aka yi tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce daga bisani wasu fararen hula 2 ma sun mutu, sanadiyyar harbin bindiga yayin da ake musayar wuta tsakanin bangarorin biyu da yammacin ranar Asabar a garin Gubio dake da nisan km 80 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

An shafe kimanin sa'o'i 5 ana musayar wutan, inda mayakan suka yi kokarin mamaye sansanin soji dake garin na Gubio, sai dai majiyar ta ce sojojin sun yi nasarar dakile yunkurin maharan.

Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ma ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa, gwamnati za ta samar da dukkan taimakon da sojojin suke bukata don tabbatar da samun nasara a kan kungiyar Boko Haram.

Shugaban 'yan sinitiri na Civilian JTF Mohammed Abdullahi, ya shaidawa Xinhua cewa, hadin gwiwarsu da sojoji ne ya kai ga nasarar da aka samu kan mayakan Boko Haram da suka tsere. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China