Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu mahara sun hallaka mutane 10 a jihar Katsina dake Najeriya
2019-07-15 20:12:39        cri

Rundunar 'yan sandan tarayyar Najeriya reshen jihar Katsina, ta ce ta gano gawawwakin mutane 10, da wasu 'yan bindiga sun hallaka, a kauyen Kirtawa, dake karamar hukumar Safanan jihar Katsina, wadda ke arewa maso yammacin kasar.

A ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gambo Isah, 'yan bindigar kan babura kimanin 300, sun kutsa kai cikin kauyen ne a daren ranar Asabar, kana suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sabbaba kisan mutanen goma, tare da jikkata wasu mutane 5, ciki hadda wani soja daya, da wani jami'in tsaron na daban. An ce maharan sun yiwa jami'an tsaron dake kokarin kare kauyen kwantan bauna.

Isah ya ce tuni aka aike da dakarun jami'an tsaro na hadin gwiwa zuwa yankin da lamarin ya faru, domin sanya ido kan yanayin da ake ciki, tare da nemo da kuma damke maharan da suka tsere.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China