Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 6 sun mutu yayin harin yankin arewa maso gabashin Najeriya
2019-08-07 20:17:04        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wata 'yar kunar bakin wake da wasu mutane biyar sun gamu da ajalinsu, biyo bayan wani harin kunar baki wake da aka kai a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno Bello Danbatta, ya bayyana cewa, wasu mutane biyar, da suka hada da 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya uku da fararen hula biyu sun jikkata a fashewar da ta auku ranar Litinin da dare a karamar hukumar Mafa dake jihar Borno.

Danbatta ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yar kunar bakin waken da ta tayar da abubuwan fashewar dake daure a jikinta, ta nufi taron jama'a dake dandalin tsakiyar garin ne. Masu aikin ceto a yankin, sun gano gawarta da na mutane biyar din da harin da ya rutsa da su.

Sai dai jami'an ba su bayyana asalin 'yar kunar bakin waken ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China