Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bunkasa tattalin arziki jigo ne wajen samun dauwamamman zaman lafiyar Afrika
2019-08-16 13:17:34        cri

Wata kwararriya kuma mai sharhi kan harkokin kasa da kasa ta ce, kamata ya yi gwamnatocin kasashen Afrika su yi kokarin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasashensu, kasancewar samun dauwamamman zaman lafiya ya ta'allaka ne kan ci gaban tattalin arziki.

Rose Fumpa-Makano, ta fada a yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ta ce babu yadda an taba samun dawwamamman zaman lafiya ba tare da samar da ingantaccen tsarin ci gaban tattalin arzikin da zai kyautata rayuwar jama'a ba.

Makano, wacce ke koyarwa a tsangayar nazarin zaman lafiya da magance rikice rikice ta kwalejin Dag Hammarskjold dake jami'ar Coppoerbelt ta kasar Zambia, ta lura cewa, nahiyar ta kasance cikin talauci ne saboda rashin cikakken aiwatar da tsare tsaren da suka shafi ci gaban tattalin arziki.

A cewarta, ba zai yiwu a samu zaman lafiya na hakika ba, muddin akwai tsananin talauci da fatara. Ta ce wannan ne dalilin da ya sa ya zama tilas a rungumi ingantaccen tsarin aiwatar da shirin raya tattalin arziki, wanda shi ne zai tabbatar da samun dauwamamman zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China