Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta yi kira ga kamfanonin mai da suka bar kasar su koma saboda kyautatuwar tsaro
2019-08-04 15:45:09        cri

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Ovie Omo-Agege, ya yi kira ga kamfanonin mai da suka bar kasar, da su koma saboda kyautatuwar yanayin tsaro a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.

Ovie Omo-Agege ya ce, komawar kamfanonin zai gaggauta ci gaban yanki da samar da aikin yi ga matasa da kuma kara tabbatar da tsaron yankin.

Kasar ta dogara ne kan kaso 70 na kudin shigar da gwamnatin ke samu daga man fetur da kuma kaso 90 na ribar da take samu daga fitar da kayayyaki zuwa ketare.

Kamfanonin dake aiki a yankin sun yi fama da matsalolin da suka hada da fasa bututun mai da satar kayayyakin aiki, a wani lokaci ma har da satar jami'ansu.

Tsagaitar hare-hare a baya-bayan nan a yankin, ya biyo bayan yunkurin gwamnatocin kasar da na jihar Rivers, na wanzar da zaman lafiya, inda tsageru sama da 22,000 suka ajiye makamansu.

Ko a watan Yunin shekarar 2009, gwamnatin kasar ta gabatar da shirin afuwa ga 'yan bindiga dake yankin Neja Delta, wadanda suka ajiye makamai a wani yunkuri na kawo karshen rashin tsaro a yankin, dake haifar da asarar biliyoyin daloli ga kasar da take kan gaba wajen sayar da man fetur ga kasashen waje a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China