Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta kai matakin wasan kusa da na karshe a gasar AFCON
2019-07-11 09:41:27        cri

Kungiyar wasan kwallon kafan Najeriya Super Eagles a daren ranar Laraba ta doke kungiyar wasan Bafana Bafana ta Afrika ta kudu da ci 2-1, lamarin da ya ba ta damar kaiwa ga matakin wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2019 (AFCON) a kasar Masar.

Dan wasan tsakiya Samuel Chukwueze, shi ne ya zura kwallon farko mintoci 27 bayan fara wasan bayan wani yunkuri na farko da ya yi na zura kwallo a ragar a yayin da mai tsaron bayan Afrika ta kudu ya tare kwallon.

Bayan shafe mintoci 70 da fara wasan, dan wasan tsakiya Bongani Zungu ya farke kwallon ga Afrika ta kudu, da farko an soke kwallon saboda zargin satar gida, daga bisani kuma bayan amfani da na'urar dake taimakawa lafari, an hakikance babu satar gida, inda aka amince da kwallon.

Ala tilas an sake kara wa'adin gasar, mai tsaron bayan Najeriya William Troost-Ekong, ya zura kwallon da ya baiwa Najeriyar nasara bayan bugun kusurwa, lamarin da mai tsaron ragar Afrika ta kudu ya kasa rike kwallon yayin da ake mintoci 89 da buga wasan.

Najeriya wacce ta dauki kofin gasar AFCON sau uku ta kai matakin wasan kusa da karshe a matsayin ta biyu a rukunin B da maki biyu bayan da ta gamu da fushin jagorar rukunin gasar AFCON kuma sabon shiga wato Madagascar, wacce za ta fafata da Tunisia ranar Alhamis a wasan kusa da na karshe.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China