Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Buhari: Afirka tana bukatar tsari a masanaantunta na samar da kayayyaki
2019-07-04 09:10:34        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, nahiyar tana bukatar manufar cinikayya da ma ajanda a masana'antun samar da kayayyaki dake nahiyar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja, babban birnin kasar, bayan da fadar shugaban kasar ta sanar da cewa, za ta sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar (AfCFTA) yayin taron kolin kungiyar tarayyar Afirka (AU) dake tafe.

Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya masu kwafe, ta ruwaito shugaba Buhari na cewa, manufar Najeriya ta shiga yarjejeniyar, ita ce, ganin an samu saukin zirga-zirgar abubuwan da aka sarrafa a nahiyar, wato kayayyaki da ayyukan hidima masu sigar nahiyar ta fannin albarkatu da inganci.

Ya ce, gwamnatin Najeriya za ta yi kokarin bullo da wasu ka'idoji da za su inganta manufofin da za su kai ga bunkasa kayayyakin da za a rika samarwa a nahiyar. Yana mai cewa, idan ba a takaika irin nau'o'in kayayyakin da za su rika shiga kasashen nahiyar ba, hakan na iya mamaye kasuwanninmu. Kuma illar ita ce, kasashen dake bakin ruwa, su ne za su amfana, yayin da kasashen da ba su da iyakokin ruwa za su ci gaba da dandana kudarsu, su ma koma dogaro ga taimako.

Najeriya, kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, tana daya daga cikin kasashen da har yanzu ba su sanya hannun kan yarjejeniyar ta AfCTFA ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China