Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An harbi akalla yan sanda 6 a birnin Philadelphia na Amurka
2019-08-15 13:23:47        cri

'Yan sanda akalla 6 ne suka ji rauni sanadiyyar harbi da yammacin jiya Laraba a birnin Philadelphia na Amurka, amma babu wanda ya ji raunin dake barazana ga rayuwarsa.

Gidan talabijin na birnin WPVI, ya ruwaito John McNesby, shugaban jami'an tsaro na birnin na cewa, 'yan sanda 6 sun ji rauni kuma suna jinya a asibitin birnin.

Harbin ya auku ne a unguwar Nicetown-Tioga na birni, a kusa da gini mai lamba 3700 dake kan titin North 15th. Wasu Hotunan da aka dauka ta sama sun nuna an girke gomman 'yan sanda dauke da manyan kayayyakin aiki a unguwar.

Wata ganau ta shaidawa gidan talabijin na WPVI cewa, an ji karar harbin bindiga akalla 100. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China