Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 20 sun mutu a harin bindiga da aka kai jihar Texas ta Amurka
2019-08-04 15:36:53        cri

Wani harin bindiga a jiya Asabar, ya yi sanadin mutuwar mutane 20 da raunata wasu 26 a jihar Texas ta Amurka.

A cewar shugaban 'yan sandan jihar Greg Allen, maharin farar fata ne mai shekaru 21, dan jihar ta Texas.

Ya kuma bayyana harin a matsayin na kiyayya. Yayin da hukumar bincike kan tsaro ta FBI, ta yi gargadin cewa akwai bukatar kara zurfafa bincike don gano ainihin yanayin laifin.

Shugaban 'yan sandan ya ce, jihar Texas za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa laifin kisan kai.

'Yan sanda sun ce, an kai harin ne wani kantin sayar da kayayyaki na Walmart, wanda ke da nisan kilomita 13 daga birnin El Paso na jihar.

A cewar hukumomin tsaro, a lokacin kai harin, kantin na cike da mutanen da suka kai 3,000, saboda shigar lokacin hada-hadar sayayyar komawa makaranta.

Wata majiya daga hukumomin tsaron ta bayyana sunan maharin a matsayin Patrick Crusius. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China