Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi zanga-zanga a gaban fadar White House don neman gwamnatin Amurka ta kayyade yawan bindigar dake hannun fararen hula
2019-08-04 16:23:01        cri

Tun bayan harin bindiga da aka kai wani kantin sayar da kayayyaki a jihar Texas ta Amurka jiya Asabar, mutane sama da dari sun taru a gaban kofar fadar White House domin neman gwamnatin kasar ta yi kokarin kayyade yawan bindigogin dake hannun 'yan kasar, ta yadda za a hana sake aukuwar makamancin harin.

Mambobin kungiyar dake rajin kayyade yawan bindigogin dake hannun fararen hula domin tabbatar da tsaron al'umma wato "Moms Demand Action" sama da dari daya, sun taru a gaban kofar fadar White House da yammacin jiya, domin nuna adawa ga gwamnati, inda suka rike takardu dauke da kalaman da suka hada da "a binciki ainihin yanayin laifin" da "kada a kara kashe wani" da "kada a yi shiru, dole a hana sake aukuwar harin bindiga".

Rahotanni sun ce, mambobin kungiyar sun yi taron shekara a Washington jiya, amma da jin labarin aukuwar harin, nan take suka yi tattaki zuwa kofar fadar White House domin nuna adawa da harin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China