Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha na maraba da masu zuba jarin Sin a fannin fasahar kiwon lafiya
2019-05-23 13:35:55        cri

Gwamnatin kasar Habasha ta bukaci kamfanonin fasaha na kasar Sin da su yi amfani da dunbun damammakin zuba jari dake kasar Habashan, musamman a fannin fasahar kiwon lafiya.

Ministan harkokin wajen kasar Habasha, Aklilu Hailemichael, shi ne ya yi kiran a lokacin ganawa da wakilan kamfanonin fasahar kiwon lafiya na kasar Sin a ranar Laraba a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

"Ma'aikatar harkokin wajen Habasha, tare da hadin gwiwar ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, suna goyon bayan kamfanonin kasar Sin su zuba jari a fannin fasahar kiwon lafiya." in ji Hailemichael.

Wakilan zuba jarin na kasar Sin, sun kumshi wakilai daga manyan kamfanonin fasahar kiwon lafiya, a lokacin tattaunawar sun lura cewa, muhimman na'urorin kiwon lafiya na zamani na kasar Sin za su taimaka wajen kokarin zamanantar da fannin kiwon lafiyar kasar Habasha, musamman wajen yaki da cutar sankara da sauran cututtuka masu nasaba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China