Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF:Kwaskwarimar da Sin take gudanarwa tana amfanawa manufar bude kofa ga ketare
2019-06-06 13:38:31        cri
Mataimakin direktan reshen hukumar kula da harkokin Asiya da Pacific na asusun ba da lamuni na duniya IMF, Kenneth Kang ya bayyana a jiya 5 ga wata a nan binrin Beijing cewa, Sin ta sa kaimi ga kwaskwarima a fannin tsare-tsaren tattalin arziki, matakin da zai ingiza manufarta na bude kofa ga ketare da habaka karfin kasuwanninta a nan gaba.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Kang ya yi bayani kan sakamako a matakin farko da ya samu cikin sharwarwari da ya yi da kasar Sin, kan aya ta hudu ta shekarar 2019, inda ya furta cewa, Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki a wannan shekara cikin karko bayan ta fuskanci sanyin jiki a bara, matakin da ya tabbatar da manufofi da masu amfani da gwamnati ke dauka.

Ya kara da cewa, Sin tana ci gaba da kwaskwarima, abin da zai kara karfinta na takarar tattalin arziki mai saukin aiwatarwa.

Aya ta hudu na nufi aya ce ta hudu bisa yarjejeniyar IMF, IMF dai ta kan tura jami'anta zuwa mambobin kasashe a kowace shekara, don tattara bayanan tattalin arziki, da hada-hadar kudi, da tattaunawa da jami'an kasar kan yadda ake bunkasa tattalin arziki da manufofin da aka tsara. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China