Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci kasashen gabashin Afrika su daidaita matakin fitar da hayaki mai gurbata muhalli
2019-06-11 15:46:00        cri

MDD ta bukaci kasashen yankin gabashin Afrika su daidaita matakin fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Rob de Jong, shugaban sashen kula da ingancin iska da sufuri na hukumar kare muhalli na MDD, ya shaidawa kasashen yankin su daina amfani da ababen hawa masu fitar da hayaki masu gurbata muhalli, maimakon haka, su komawa ababen hawa da ba sa fidda hayaki.

Rob de Jong ya shaidawa wakilan dake halartar taron karawa juna sani na hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika (ECA) kan daidaita matakin fitar da hayaki mai guba cewa, akwai bukatar samar da ingantacciyar dabarar da za ta tabbatar da yankin na da iska mai tsaro da inganci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China