Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan wajen Sin ya aikawa takwaransa na Masar sakon ta'aziyya dangane da harin ta'addancin da aka kai Alkahira
2019-08-08 20:39:13        cri

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya aikawa takwaransa na kasar Masar Sameh Shoukry sakon ta'aziyya, dangane da mutanen da aka kashe a harin ta'addanci na baya-bayan da aka kai Alkahira, babban birnin kasar ta Masar.

A cikin sakon, Wang ya jajantawa wadanda suka jikkata da ma iyalan wadanda harin ya rutsa da su.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China