Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an tsaron Najeriya sun dakile yunkurin zanga zangar juyin juya hali da wasu suka shirya
2019-08-06 09:36:46        cri
A jiya Litinin jami'an tsaron Najeriya suka dakile yunkurin zanga zangar da wasu bata gari suka shirya da nufin kifar da gwamnati, bisa zargin da suka yi na rashin gamsuwa da yadda gwamnatin kasar ke tafiyar da salon shugabancinta.

Jami'an tsaro dauke da kayan aiki sun bazu a sassan kasar, inda suka tsaurara tsaro a yankunan da ake fargabar masu zanga zangar zasu yi gangami, tsohon dan takarar neman shugabancin kasar ne yayi yunkurin shirya zanga zangar.

A martanin data mayar, gwamnatin Najeriya tace hanyar kadai da ake bi wajen sauya gwamnati a tsarin mulkin demokaradiyya shi ne ta hanyar zabe.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya bayyana cewa, a koda yaushe gwamnati tana maraba da 'yan kasa su gudanar da zanga zangar lumana domin bayyana bacin ransu ga gwamnati, amma a cewarsa zanga zangar lumana ta sha bamban da yunkurin kifar da gwamnati.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China