![]() |
|
2019-08-07 14:23:24 cri |
Kwanan baya, gwamnatin Amurka ta sanar da shirin kara bugawa kayayyaki Sin dake shiga Amurka karin harajin kwastam na kashi 10 cikin dari, wadanda darajar su ta kai dala biliyan 300, matakin da ya sabawa matsaya daya da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma a taron G20 da aka yi a Osaka na kasar Japan a watan Yunin da ya gabata.
A hannu guda, kwamiti mai kula da aikin haraji na majalisar gudanarwar kasar Sin bai gabatar da tabbaci kan ko za a buga karin haraji kan kayayyaki da ake sayowa daga Amurka bayan ran 3 ga wata ba ko a'a, sai kuma wasu kamfanonin kasar Sin da lamarin ya shafa, sun fara dakatar da sayo kayayyakin amfanin gona daga Amurka.
Sanarwar ta ce, masanan tattalin arziki na kungiyar sun nuna cewa, a shekarar 2017, yawan kudin da Amurka ta samu ta fuskar fitar da hajojin ta na amfanin gona zuwa kasar Sin ya kai dala biliyan 19.5. A kuma shekarar 2018, wannan adadi ya ragu zuwa dala biliyan 9.1. Kana ya sake raguwa da dala biliyan 1.3 a shekarar nan ta 2019, matakin da ya sa Amurka za ta fuskanci hadarin rashin damar shiga kasuwannin kasar Sin.
Sanarwar ta ce, shirye-shiryen ba da taimako ga manoma, da hukumar aikin noma ta kasar Amurka ta gabatar, ba su da amfani cikin dogon lokaci, kuma kungiyar ta bukaci tawagogin bangarorin biyu masu kula da aikin shawarwari, da su kai ga cimma matsaya daya ba da bata lokaci ba, don tabbatar da fitowar kayayyakin gona na Amurka. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China