Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kira taron sada zumunta tsakanin biranen Sin da Amurka karo na 4
2019-07-18 19:49:31        cri

A Jiya Laraba ne aka kaddamar da bikin bude babban taron sada zumunta, tsakanin biranen kasashen Sin da na Amurka karo na hudu a birnin Houston na Amurka. A yau kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai cewa, yana sa ran babban taron zai ciyar da huldar hadin gwiwar sada zumunta dake tsakanin kasashen biyu gaba yadda ya kamata.

Lu Kang ya kara da cewa, wakilai sama da 200, daga hukumomin gwamnatocin kasashen biyu, da kungiyoyi masu zaman kansu sun halarci taron, inda suka yi tattaunawa kan yadda za su kara karfafa hadin gwiwa, da cudanya tsakanin sassan biyu a nan gaba. Haka kuma, sun kira taron kungiya kungiya, domin tattauna batutuwan dake shafar gina biranen zamani, da hanyar siliki kan teku, da gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin manyan biranen kasashen biyu, da kara karfafa cudanyar ba da ilmi da sauransu.

Lu Kang ya jaddada cewa, kara karfafa fahimtar juna, da zumunta dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu, tushe ne na tabbatar da ci gaban hulda mai dorewa tsakanin Sin da Amurka. Ya ce kawo yanzu, gaba daya birane 227 na sassan biyu sun riga sun daddale huldar sada zumunta dake tsakaninsu. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China