Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawanyen 'yan adawa a Sudan sun amince su tattauna da TMC
2019-07-04 11:10:25        cri

Rahotanni daga kasar Sudan na cewa, kungiyoyin 'yan adawa na Freedom Opposition da Change Alliance sun amince su tattauna kai tsaye da majalisar soji ta wucin gadin kasar(TMC).

Kusa a kawancen 'yan adawar Madani Abbas Madani ya shaidawa taron manema labarai a Khartoum, babban birnin kasar cewa, kungiyoyin sun gana inda suka yanke shawarar amsa gayyatar tattaunawar kai tsaye da jagororin sojin kasar.

Ya kara nanata muhimmancin sake nuna yarda tsakanin sassan biyu ta hanyar abin da ya kira, ka'idoji ciki har da sakin wadanda ake tsare da su, dawo da layin Intanet da kafa kwamitin bincike game da abubuwan da suka fara na tarwatsa wurin da masu bore ke zaman dirshan dake gaban hedkwatar sojan kasar.

A ranar Talata ce kungiyar tarayyar Afirka da kasar Habasha suka gayyaci sassan biyu, don yin wata ganawa a jiya Laraba, inda za su tattauna batutuwan da sassa biyu suka sha banban a tattaunawar da suka yi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China