Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan bindiga sun yi awon gaba da 'yan kasuwa 18 a Najeriya
2019-07-24 20:08:14        cri
Hukumomin 'yan sanda a Najeriya sun bayyana a yau Laraba cewa, sun kaddamar da binciken gano 'yan kasuwa a kalla 18 da wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a jihar Nijar dake yankin tsakiyar kasar.

Rundunar 'yan sandan jihar Neja inda lamarin ya faru ranar Asabar din da ta gabata, ta bayyana cewa, wata tawagar bincike ta musamman da ta kafa, ta fara aiki don gano mutanen da aka sace.

Majiyoyi daga yankin na cewa, 'yan kasuwar sun taso ne daga garin Pandogari a karamar hukumar Rafi cikin wata motar bas mai daukar mutane 18 a kan hanyarsu ta zuwa kauyen Bassa dake karamar hukumar Shiroro na jihar Nejar, inda 'yan bindigar suka tsare motar da suke ciki a karshen makon da ya gabata. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China