Yawan kudin da kamfanonin yanar gizo suka samu a watanni 6 na farkon bana ya karu da kashi 17.9 cikin dari a kasar Sin
Ma'aikatar harkokin masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta sanar a jiya cewa, an raya sha'anin yanar gizo ta Internet da hidimar da aka bayar ta yanar gizo a kasar Sin a watanni 6 na farkon bana yadda ya kamata, inda yawan kudin da aka samu daga wannan sha'ani ya karu da kashi 17.9 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Haka kuma, an kara zuba jari a bangaren nazarin harkar yanar gizo. A cikin watanni 6 na farkon bana, yawan jarin da aka zuba a wannan sha'ani ya kai Yuan biliyan 23, wanda ya karu da kashi 29.4 cikin dari. (Zainab)
Labarai masu Nasaba