Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta ci gaba da girmama huldar kasa da kasa
2019-07-31 10:39:55        cri
A ranarsa ta farko da kama aiki a matsayin zaunannanen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya yi alkawari a Hedkwatar Majalisar dake New York na Amurka cewa, Kasar Sin, daya daga cikin mambobin kwamitin sulhu na MDD na dindin-din, za ta ci gaba da girmama huldar kasa da kasa da mara baya ga muhimmiyar rawar da MDD ke takawa.

Zhang Jun, ya ce kasar Sin za ta yi cikakken amfani da damarmakinta a mastayin mambar dindin-din ta kwamitin sulhu na MDD, da girmama ka'idoji da manufofin Majalisar, da kuma shiga a dama da ita cikin harkokin kasa da kasa, da inganta sulhu ta hanyar siyasa da diflomasiyya da kuma bada gudunmuwa ga cimma zaman lafiya a duniya.

Har ila yau, ya ce kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa da kasa da kasa domin magance kalubalen da duniya ke fuskanta bisa hanyar da ta dace.

Kafin kira taron manema labarai da 'yan jaridun kasar Sin, Zhang Jun, ya gabatar da takardar nadinsa ga Sakatare Janar na majalisar, Antonio Guterres. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China