Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar kasar Sin ta kara bude kofa ta zo kan gaba, in ji wani masanin tattalin arziki
2019-07-25 10:51:05        cri
Shaihun malami a kwalejin koyar da ilimin cinikayya da jagoranci ta Frankfurt dake kasar Jamus farfesa Horst Loechel, ya ce sanarwar da mahukuntan kasar Sin suka yi, game da aniyar kasar na kara bude kofa a fannonin hada hadar kudade ga masu sha'awar zuwa jari daga ketare, mataki ne da ya zo a lokacin da ake bukatar sa. Farfesa Loechel ya ce matakin zai amfani Sin da ma sauran sassan duniya baki daya.

Masanin tattalin arzikin ya bayyana hakan ne, yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Laraba, inda ya ce matakin dage takunkumi a fannonin hada hadar hannayen jari, da sarrafa kudade ga kamfanoni masu jarin waje nan da shekarar 2020, zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa yaduwar jarin kudade da Sin ke samu.

Ya ce ko da yake matakin ya zo shekara guda kafin lokacin da aka ayyana a baya, duk da haka zai haifar da da mai ido ga tattalin arzikin kasar.

Farfesa Horst Loechel ya kara da cewa, Sin ta dade da alkawarta ci gaba da aiwatar da sauye sauye, da kara bude sasssan ta na cinikayya da kasuwanci. A kuma wannan mako, cibiyar hada hadar hannayen jari mai amfani da fasahohin zamani ta STAR, ta shiga kasuwar hannayen jari ta Shanghai, wanda hakan ya karfafa nasarar sauye sauye da Sin ke aiwatarwa a fannin kasuwannin hannayen jarin ta (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China