Friday    Apr 25th   2025   
in Web hausa.cri.cn
An bude bikin nune-nunen tufaffi da kayan saka na Sin karo na 20 a birnin New York
2019-07-23 16:23:16        cri

 

 

An bude bikin nune-nunen tufaffi da kayan saka na Sin karo na 20 a cibiyar Javits dake birnin New York a jiya.

Mataimakin shugaban kungiyar masana'antun saka ta kasar Sin kuma shugaban sashen kula da sha'anin saka na kwamitin sa kaimi ga cinikin dake tsakanin kasa da kasa na kasar Sin Xu Yingxin ya bayyana cewa, bana ta cika shekaru 20 da fara gudanar da bikin nune-nunen. A matsayin kasa mafi samarwa da fitarwa da kuma sayon tufaffi da abin saka a duniya, masana'antun saka na kasar Sin ya zama muhimmin dandalin sa kaimi ga hadin gwiwar tattalin arziki da al'adu dake tsakanin kasa da kasa da sarrafa harkokin duniya. Kamfanonin samar da kayan saka da tufaffi na kasar Sin da dama sun fadada idanunsu ta hanyar wannan biki, da fara gudanar da ayyukansu a kasar Amurka, inda daga baya za a watsa su a fadin duniya. Hakan ya nuna goyon baya ga sa kaimi ga sha'anin saka na Sin, ta yadda zai fita waje, ya kuma kyautata tsarinsa.

An ce, kamfanoni kimanin 800 daga kasashe da yankuna 17 sun halarci bikin nune-nunen a birnin New York a wannan karo. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China