![]() |
|
2019-07-08 13:26:45 cri |
An ce, a farkon rabin shekarar bana, Sin ta cimma burin rage lokacin bude sabbin kamfanoni zuwa kwanaki 8 da rabi, kana an kyautata tsarin rufe kamfanoni, don haka kamfanoni dubu 717 da dari 9 na kasar Sin sun janye daga kasuwa ta hanyar masaukin tsarin rufe su. Tun daga shekarar bana, hukumomin sa ido ga kasuwa na kasar Sin sun kara gudanar da ayyukansu a kasuwa, da yin kwaskwarima kan tsarin bada iznin shigar da kamfanoni a cikin kasuwa, da kara sa ido ga kasuwa bisa dokoki don samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasar. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China