Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe sojoji 2 da yin garkuwa da wani dan kasar waje a kudancin Najeriya
2019-07-19 11:11:33        cri
Hukumar yan sanda a Najeriya tace wasu 'yan bindiga da ba'a tantance su ba sun hallaka sojoji biyu da kuma yin garkuwa da wani dan kasar waje bayan da suka datse wani wajen da ake gudanar da aikin gina titin mota a kudancin kasar.

'Yan sandan sun ce, al'amarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba a kusa da karamar hukumar Ukanafun dake jahar Akwa Ibom, a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Kawo yanzu, 'yan sandan ba su tabbatar da kwararren injiniyan da aka sace ko dan wace kasa ba ne.

Sojojin biyun dai suna yin rakiya ne ga injiniyan a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin gina titin mota a kauyen Inen Ekeffe dake jahar, a daidai lokacin 'yan bindigar suka bude wuta a wajen.

Wata majiya daga yankin ta ce, 'yan bindigar sun yi awon gaba da bindigogin sojojin bayan sun hallaka su.

Obong Johnson Obosi, shugaban kauyen Inen Ekeffe, ya ce, wasu dakarun sojoji daga wani barikin soji dake kusa da yankin sun kawo dauki jim kadan bayan afkuwar lamarin inda suka kwashe gawarwakin takwarorin nasu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China