![]() |
|
2019-07-22 10:51:07 cri |
Yawan mata masu gabatar da kara a kotu a kasar Sin ya kai 23,540, adadin da ya tasamma kashi 34.9 bisa 100 na yawan jami'an gabatar da kara a kotu dake kasar Sin baki daya, kamar yadda kungiyar mata masu gabatar da kara a kotu ta kasar Sin (CWPA) ta sanar.
Kungiyar ta CWPA ta ce, mata masu gabatar da kara a kotu sun taka muhimmiyar rawa wajen dakile munanan laifuka, kana adadin mata masu gudanar da wannan aiki a sassa daban daban na kasar yana ci gaba da karuwa.
A cewar kungiyar, a bisa irin kokarin da mata masu gabatar da kara a kotu suke yi, ayyukan gabatar da kara a kotu da suka shafi matasan da shekarunsu ba su kai 18 a duniya ba suna matukar samun tagomashi.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China