Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan cinikayyar da aka yi tsakanin lardin Gansu da kasashen dake aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" ya zarce Yuan biliyan dari
2019-07-22 14:02:54        cri
An yi taron karawa juna sani kan shawarar "ziri daya da hanya daya" tsakanin kwararru da masana da kafofin watsa labarai na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin da cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Belarus.

Wani jami'in kwamitin neman ci gaba da yin gyare-gyare na lardin Gansu Ju Long ya bayyana cewa, kudin cinikin kayan da aka yi tsakanin Gansu da kasashen dake aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" ya zarce Yuan biliyan dari, kuma Gansu ta kafa wasu ofisoshin kasuwancinta guda 12 a wadannan kasashe. Ya zuwa yanzu, lardin Gansu yana gudanar da cinikayya tare da kasashe da yankuna sama da 180 a duk fadin duniya.

Kawo yanzu, lardin Gansu ya kulla zumunci da birane da garuruwa da dama a kasashen dake aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", inda suke kara mu'amala da cudanya tsakanin manyan jami'an gwamnati da yin cudanyar tattalin arziki da kasuwanci da kuma al'adu, kuma hadin-gwiwarsu ta fannonin ilimi da kiwon lafiya da magunguna da muhallin halittu na kara inganta.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China