Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mutane 8 a yanki mai magana da yaren Turanci a Kamaru
2019-06-09 16:01:58        cri
Hukumomi sun tabbatar da cewa mutane 8 ne aka kashe kana wasu mutane da dama suka jikkata a ranar Asabar a yankin Ekona, wani karamin kauye ne dake shiyyar kudu maso yammaci, wato guda daga cikin yankuna biyu na jamhuriyar Kamaru masu magana da yaren Turanci dake fama da yawan tashin hankali.

"Ni da kaina na ga gawarwakin mutane 8, kusan dukkaninsu maza ne sai mace guda daya. Suna kwance a cikin daji. Dukkansu an harbe su ne daga waje marar nisa," wani mazauni yankin wanda ya bukaci a sakaye sunansa shi ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

An samu rahotanni dake cin karo da juna game da ainihin mutanen da aka hallaka. 'Yan awaren masu dauke da makamai suna ikirarin cewa wadanda aka hallaka din fararen hula ne, wadanda dakarun gwamnati suka harbe su, amma sojojin sun ce 'yan awaren ne aka kashe a lokacin da dakarun suka yi kokarin dakile hare-haren 'yan awaren.

"Dakarun sojoji sun samu bayanan sirri game da zuwan 'yan ta'adda masu yawa na 'yan awaren zuwa yankin, inda kuma suka bude musu wuta a daidai lokacin da suke kan hanyarsu ta kai hari a wani kauye. Sun bude wuta yayin da suka fahimci inda muke, mu ma muka mayar musu da martani. Mun yi nasarar kwantar da kusan mutane 10 daga cikinsu, kana sauran kuma sun tsere da munanan raunuka," wani jami'in soja da ya bukaci a sakaye sunansa ne ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China